Isa ga babban shafi
Amurka-Korea ta Arewa

Jakadan Amurka ya isa Korea ta kudu kan tattaunawar Trump da Kim

Ganawar shugaban Amurka Donald Trump da na Korea ta Arewa Kim Jong-un ranar 12 ga watan Yunin bara a kasar Singapore
Ganawar shugaban Amurka Donald Trump da na Korea ta Arewa Kim Jong-un ranar 12 ga watan Yunin bara a kasar Singapore AFP/Saul Loeb

Jakadan Amurka na musamman da ke shiga tsakani game da tattaunawar kasar da Korea ta arewa Stephen Biegun ya isa korea ta kudu don ganawa da shugaban kasar dangane da ganawar shugaba Trump da Kim cikin watan nan.

Talla

Manufar ziyarar ta Mr Stephen Biegun a Korea ta kudu bai wuce share fagen tattaunawar shugaban Amurka Donald Trump da Kim Jong Un na Korea ta arewa ba, wadda ita ce karo na biyu duk dai karkashin shirin Amurkan na ganin Korea ta ajje shirinta na kera makaman nukiliya.

Kamfanin dillacin labaran Korea ta kudu Yonhap ya shaida cewa yayin ziyarar ta Mr Stephen, bangarorin biyu za su fitar da jadawalin wuri, lokaci da kuma ranar da za a yi ganawar ta Trump da Kim.

Ma’aikatar harkokin wajen Korea ta Kudu ta ce Mr Stphen zai gana da babban mashawarcin gwamnatin Korea ta kudun kan harkokin tsaro Chung Eui-yong a gobe litinin gabanin tafiyarsa kauyen Panmunjom inda a nan ne zai gana da wakilan korea ta arewan.

Stephen Biegun wanda ya samu tarba daga fadar shugaban korea ta kudu, sun tattauna game matakin da Korea ta arewan ta ke game da shirinta na lalata makamanta na nukiliya.

Da ma dai kamar yadda ya alkawarta a makon nan ne shugaba Trump na Amurka ya ce zai sanar da rana, lokaci da kuma wurin da za su gana da mai girma Kim Jong Un kamar yadda ya furta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.