Isa ga babban shafi
Trump-Kim

Trump zai gana da Kim a birnin Hanoi na Vietnam

Ganawar tsakanin ranakun 27 zuwa 28 ga watan nan ita ce irinta ta biyu da shugabannin biyu za su yi bayan ta watan Yunin bara a Singapore
Ganawar tsakanin ranakun 27 zuwa 28 ga watan nan ita ce irinta ta biyu da shugabannin biyu za su yi bayan ta watan Yunin bara a Singapore REUTERS/Jonathan Ernst/File Photo

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da birnin Hanoi na kasar Vietnam a matsayin wurin da zai gana da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un ranar 27 zuwa 28 ga watan nan.

Talla

Ganawar shugabannin biyu nan da 'yan kwanaki ana saran za ta mayar da hankali kan matakan da Korea ta arewa ke bi wajen kawo karshen shirinta na nukiliya baya ga lalata makaman da ta mallaka.

Cikin sakon da Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce tuni jami’ansa na musamman suka gana da jami’an Korea game da ganawar kuma tuni suka amince da wuri da lokaci.

A watan Yinin bara ne Donald Trump ya yi ganawa ta farko da Kim Jong Un a Singapore, ganawar da ta kawo akrshen musayar zafafan kalamai tsakanin shugabannin biyu masu tsohuwar gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.