Isa ga babban shafi
Australia

Kotu ta samu limamin coci da laifin lalata da yara

George Pell
George Pell AAP Image/Erik Anderson/via Reuters

Wata Kotu a Australia ta samu wani babban limamin darikar Katolika kuma daya daga cikin masu bada shawara na kusa da Fafaroma Francis, George Pell da laifin cin zarafin wasu kananan yara biyu.

Talla

Masu taimakawa alkali yanke hukunci sun samu Pell da laifin lalata da kuma cin zarafin yaran biyu da ke Mujami’ar St. Patrick a Melbourne a shekarar 1990.

Pell mai shekaru 77 shi ne mai rike da mukami mafi girma da aka taba samu da irin wannan laifi a gaban kotu.

Ana sa ran Me. Pell zai fara fuskantar hukunci daga ranar Laraba . Kodayake ya kaddamar da daukaka kara domin kalubalantar tuhumar da ake yi masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.