Isa ga babban shafi

Manyan kasashe sun haramtawa jirgin Boeing 737 keta sararin samaniyarsu

Yanzu haka dai ana ci gaba da bincike don gano musabbabin hadarin jirgin na Ethiopia a safiyar shekaran jiya lahadi
Yanzu haka dai ana ci gaba da bincike don gano musabbabin hadarin jirgin na Ethiopia a safiyar shekaran jiya lahadi REUTERS/David Ryder

Manyan kasashen duniya ciki har da Faransa da Birtaniya da Jamus da kuma Holland da China sun haramtawa jirgin Boeing samfurin 737 Max 8 kirar Amurka keta sararin samaniyarsu, matakin da ke matsayin martini kan hadarin jirgin da ya hallaka mutane 157.

Talla

Australia wadda a yau Laraba ta fitar da sanarwar haramtawa zirga-zirga da jirgin, ma'aikatar da ke kula da sararin samaniyar kasar ta ce suna da jirgin da zai maye gurbin jigilar da jirgin na Boeing ke musu.

Ita ma dai Indonesia ta bi sahun kasashen inda ta dakatar da jiragen kirar Boeing 11 tashi daga filayen jirginta, inda ta ce jiragen za su ci gaba da zama a ajje har zuwa lokacin da za ta gamsu da lafiyar hada-hadar jirgin a sassan duniya.

Akwai kuma kasashen Ireland da Malaysia da Mangolia da Singapore wadanda suma suka dauki makamancin matakin na dakatar da aiki da nau'in jirgin yayinda Oman wadda itama ta bi sahun dakatar da zirga-zirga da nau'in jirgin wanda ta ce har sai zuwa lokacin da za ta bayar da sanarwa ne za a ci gaba da amfani da nau'in jirgin.

Akwai kuma kasashen Argentina Mexico da Afrika ta kudu ka na Korea ta kudu da Ethiopia baya ga Brazil da kuma Norway da Turkiya India da hadaddiyar daular larabawa da Italiya wadanda dukkaninsu suka hana amfani da nau'in jirgin na wucin gadi.

A bangare guda kasar Rasha ta ce ta na ci gaba da bincike kan musabbabin hadarin amma har yanzu ba ta samu umarnin da ke nuna mata ta dakatar da amfani da nau'in jirgin ba.

Tuni dai kasar Amurka wadda ke sarrafa nau'in jirgin wanda shi ne mafi girma kuma mafi samun kasuwa a duniya ta ce ba za ta dauki kowanne irin mataki a halin yanzu ba, har sai ta samu kwararan hujjoji da ke nuna cewa hadarin na da alaka da gazawar jirgin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.