Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha-China

Amurka na zargin Rasha da China wajen haddasa rikici a sararin samaniya

Amurkan ta ce ta na da tantama kan shirin na China da Rasha la'akari da yadda Rasha ke matsayin shun gaba wajen kera makamai masu kakkabo makamai a duniya
Amurkan ta ce ta na da tantama kan shirin na China da Rasha la'akari da yadda Rasha ke matsayin shun gaba wajen kera makamai masu kakkabo makamai a duniya NASA / SpaceX

Kasar Amurka ta zargi kasashen Rasha da China wajen shirin haifar da rikici a sararin samaniya ta fuskar kera makaman harbor tauraron dan adam.

Talla

Yayin gudanar da wani taron masana daga kasashe 25 kan yadda za’a tabbatar da zaman lafiya a sararin samaniya, wanda ya samu halartar wakilai daga kasashen Amurka da China da Rasha, Mataimakin Sakataren harkokin wajen Amurka, Yleem Poblete ya bayyana shakku kan hadin kan China da Rasha.

Jakadan ya ce ta ya ya za su amince Rasha da gaske ta ke wajen dakile yaduwar makamai a sararin samaniya, alhalin su su ke kera sabbin makamai masu linzami da ke kakkabo jirage da tauraron dan adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.