Isa ga babban shafi
Amurka

An gabatar da rahoton kutsen Rasha a zaben Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana rahoton katsalandan din Rasha a matsayin bita da kullin siyasa
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana rahoton katsalandan din Rasha a matsayin bita da kullin siyasa REUTERS/Yuri Gripas

Lauyan nan na musamman, Robert Mueller ya gabatar da rahotonsa kan zargin katsalandan din Rasha a lokutan yakin neman zaben Amurka na 2016 da zummar taimaka wa shugaba Donald Trump samun nasara.

Talla

Yanzu haka, Ministan Shari’a na kasar, William Barr zai gabatar da rahoton ga Majalisar Dokokin Amurka bayan kammala nazari akai.

A cikin wata wasika da ya aika wa shugabannin Majalisar Dokokin, Mr. Barr ya shaida musu cewa, yana sa ran gabatar da musu da muhimman abubuwan da rahoton ya kunsa a wannan makon mai karewa.

Ana sa ran rahoton zai fayyace matakin da ya dace a dauka kan wadanda ke da hannu a katsaladan din.

Shugaba Trump da sauran mambobin jam’iyyar Republican sun sha bayyana binciken rahoton a matsayin bita da kullin siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.