Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta gana da Turai kan barazanar Iran

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo a birnin Brussels
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo a birnin Brussels JOHN THYS / AFP

Sakataren Harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya kai ziyarar gaggawa zuwa birnin Brussels domin ganawa da shugabannin wasu manyan kasashen Turai dangane da yadda alakar Amurka da Iran ke dada yin tsami.

Talla

Pompeo ya ziyarci Brussels ne sa’o’i kalilan bayan harin zagon-kasa da aka kaiwa wasu jiragen dakon mai na Saudiya a gabar ruwan Hadaddiyar Daular Larabawa, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar sabon rikici a yankin gabas ta tsakiya.

Mafi akasarin shugabannin kasashen Turai sun fusata da matakin Amurka na kakaba karin takunkuman karayar tattalin arziki kan Iran a dalilin takaddama kan yarjejeniyar nukiliyar kasar da manyan kasashen duniya, wadda a shekarar bara Amurka ta fice daga cikinta.

Da fari dai kasashen Kungiyar Tarayyar Turai, sun tsara tattaunawa kan wasu batutuwa da suka shafi nahiyar ce a taron na ranar Litinin, kamar zaben kungiyar da ke tafe da kuma batun ficewar Birtaniya daga cikinsu, amma tilas suka maida hankali kan yadda za su ceci yarjejeniyar nukiliyar Iran daga rushewa, la’akari da tada jijiyar wuya da ke dada zafafa tsakanin Amurka da kasar ta Iran.

A game da haka ne kuma Mike Pompeo ya zabi soma tsayawa a Brussels don ganawa da shugabannin EU, maimakon isa birnin Moscow, kafin karasawa Sochi don ganawa da shugaban Rasha Vladmir Putin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.