Isa ga babban shafi
India

India ta dau mataki dangane da guguwar Vayu

Guguwar da ta afkawa kasar India a shekara ta 2018
Guguwar da ta afkawa kasar India a shekara ta 2018 (Foto: Reuters)

Hukumomin Kasar India zasu kwashe akalla mutane 300,000 daga Jihar Gujurat dake yankin yammacin kasar domin kaucewa wata mahaukaciyar guguwa da ake saran zata sauka gobe alhamis.

Talla

JN Singh, wani babban jami’in gwamnati yace hukumar dake kula da muhalli ta tabbatar da cewar guguwar da aka yiwa lakabi da Vayu zata sauka ne gobe da safe.

Jami’in yace hasashen su ya nuna cewar guguwar zata sauka a yankuna 10 dake dauke da mutane 291,000, wanda ya zama dole a kwashe su domin kai su matsugunai 67 dan kaucewa guguwar.

A watan Mayu shekarar 2018 wata mahaukaciyar guguwa da ta ratsa yankin arewacin India, ta hallaka akalla mutane 95, tare da jikkata wasu 143, yayinda guguwar ta tumbuke bishiyoyi da kuma rusa gine-gine masu yawan gaske.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.