Isa ga babban shafi
Iran-Turai

Iran na tattaunawa da wakilan Turai kan yarjejeniyar nukiliyarta

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani Official President website/Handout via REUTERS

Mataimakin Ministan harkokin wajen Iran Abbas Aragchi ya gana da mataimakin babban jami’in diflomasiyar kungiyar kasashen Turai, Helga Schamid domin tattauna makomar yarjejeniyar nukiliyar kasar, a daidai lokacin da ake samun tankiya tsakanin Iran da Amurka.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce taron jami’an biyu da akayi a Tehran ya mayar da hankali ne kan yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2015 da kuma matsalolin da suka shafi Yankin tekun Fasha da duniya baki daya.

Ita dai kungiyar Turai na cigaba da goyan bayan yarjejeniyar da Amurka ta yi watsi da ita, yayin da Iran ke barazanar ficewa saboda yadda Amurkar ke cigaba da sanya mata takunkumi.

Ziyarar Schmid na zuwa ne kasa da mako guda bayan ziyarar ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas da Firaministan Japan Shinzo Abe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.