Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Iran ta tafka babban kuskuren kakkabo mana jirgi- Trump

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Carlos Barria

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar Iran ta yi babban kuskure wajen kakkabo jirgin kasar, yayin da ya tura mai bashi shawara kan harkokin tsaro zuwa Israila domin tattauna matakan da zasu dauka.

Talla

Shugaban Donald Trump ya shaidawa manema labarai cear ba’a karamin kuskure Iran ta tafka ba wajen kakabo jirgin mai sarrafa kan sa, inda ya kara da cewa zasu dauki mataki mai karfi kan lamarin.

Wannan martani na zuwa ne a daidai lokacin da fadar shugaban Amurkar ta bayyana cewar mai baiwa Trump shawara kan harkokin tsaro, John Bolton zai tafi Israila domin tattauna matsalolin da suka shafi tsaro a Yankin Gabas at Tsakiya tare da wakilan kasashen Rasha da Israila.

Ita kuwa kasar Iran tace zata je Majalisar Dinkin Duniya domin gabatar da shaidar dake nuna cewar jirgin da ta harbo ya shiga cikin sararin samaniyar ta ne.

Ministan harkokin wajen Iran, Javad Zarif yace zasu gabatarwa da Majalisar wanan barazanar wadda ke nuna yadda Amurka ke karya domin tinzira yaki a yankin.

Kungiyar kasashen Turai ta bukaci taka tsan tsan kan lamarin, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tura wakili na musamman Iran domin rage tankiyar da ake samu tsakanin kasar da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.