Isa ga babban shafi
Amurka

Dole na jinjinawa Amurkawa-Trump

Shugaban Amurka Donald Trump. a lokacin bikin ranar 4 ga watan Yuli
Shugaban Amurka Donald Trump. a lokacin bikin ranar 4 ga watan Yuli REUTERS/Joshua Roberts

Shugaban Amurka Donald Trump ya jinjinawa rundunar sojin kasar da zaratan Amurkawan da suka taimaka wajen gina kasar su shekaru 250 da suka gabata, lokacin da yake jawabi a wajen bikin ranar yancin kasar da ya hada da faretin soji.

Talla

Trump wanda ke jawabi a gaban mutumin mutumin tsohon shugaban kasar Abraham Lincoln, ya bayyana Amurka a matsayin gagarumar kasa, inda yake cewa kasar zata ci gaba da taka gaggaruma rawa don tabbatar da demokkuradiya da kuma kare incin Amurkawa a Duniya.

Bikin ya hada da shawagin jiragen yaki, yayin da shugaban ke cewa kasar zata cigaba da samun galaba kan shugabannin kama karya da kuma yin fice a bangaren kimiya, domin kuwa Amurkawa ke da makoma mai kyau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.