Isa ga babban shafi
Turkiya

Cinikin makaman S-400 ya tabbata tsakanin Turkiya da Rasha

Makami mai linzami da ke cin dogon zango kirar S-400 da Turkiya ta saya daga Rasha.
Makami mai linzami da ke cin dogon zango kirar S-400 da Turkiya ta saya daga Rasha. REUTERS/Vitaly Nevar

Ma’aikatar tsaron Turkiya ta fara karbar muggan makamai masu linzami kirar Rasha S-400 wadanda ta saya daga kasar ta Rasha.

Talla

Matakin dai ya harzuka Amurka da Kungiyar NATO, abinda kuma ka iya haddasa bacin dangantaka tsakanin Turkiya da Amurkan.

Amurka dai ta dade tana gargadin Turkiya kan cinikin makaman amma shugaba Erdogan yayi watsi da barazanar.

Kungiyar Tsaro ta NATO da ke ganin Turkiya na daya daga cikin mambobinta, ta nuna rashin jindadi dangane da cinikin makaman.

Amurka ta ce idan har Turkiya ta mallaki makaman kirar S-400 babu shakka sirrin irin nata makaman na cikin hadari domin ana iya satar bayanansa don amfanin Rasha.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.