Isa ga babban shafi
Amurka

Ban wanke Trump ba a zargin katsalandan din Rasha- Mueller

Robert Mueller
Robert Mueller SAUL LOEB / AFP

Shugaban Kwamitin Bincike na musamman kan zargin katsalandan din Rasha a zaben Amurka na 2016 Robert Mueller ya ce,  shi bai wanke shugaba Donald Trump daga zargin katsalandan din ba. 

Talla

Watanni 3 bayan gabatar da rahotan bincikensa kan zargin da ake yi wa kasar Rasha na katsalandan lokacin zaben na Amurka,Mueller ya sha tambayoyi daga 'yan Majalisun Amurka a wannan Larabar kan aikin da ya yi da kuma rahotan da ya gabatar.

Yayinda shugaba Trump ke cewa rahotan ya wanke shi, a bangare daya kuma 'yan Majalisun Jam’iyyar Democrat na cewa, rahotan ya bada damar tsige shugaban, Robert Mueller ya ce, har yanzu yana kan bakarsa dangane da rahotan binciken da ya gabatar, kuma ko da wasa bai wanke shugaba Trump daga tuhumar da ake masa na cewar ya nemi yin katsalandan lokacin gudanar da binciken ba.

Mueller ya kara da cewar, sun yi amfani da manufofin ma’aikatar shari’a ne wajen kauda da shakku da kuma kare hakkin kowanne dan kasa wajen kin bayyana karara cewar shugaban kasar ya aikata laifi, inda suka bar wa ma’aikatar shari’a hurumin yin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.