Isa ga babban shafi
Amurka-Facebook

Hukumar kasuwancin Amurka ta ci tarar Facebook dala biliyan 5

Amurkan dai ta zargi Facebook da gaza kare bayanan sirrin jama'a
Amurkan dai ta zargi Facebook da gaza kare bayanan sirrin jama'a ©REUTERS/Dado Ruvic/Illustration/File Photo

Hukumar da ke kula da kasuwanci a Amurka ta ci tarar kamfanin Facebook na kudi Dala biliyan 5 saboda kaucewa ka’idar aiki da kuma matsalolin da suka shafi bayanan asirin masu amfani da shi.

Talla

Hukumar kula da kasuwanci ta bayyana cewar wannan tara mai yawa na Dala biliyan 5 da aka dorawa kamfanin Facebook shine irin sa na farko da aka taba dorawa wani kamfani saboda sabawa dokokin kare bayanan asirin jama’a da gwamnatin Amurka ta taba yi.

Bayan wani zaman sulhu da akayi tsakanin bangarorin biyu, hukumar tace an bukaci Facebook ya kafa kwamitin asiri a cikin kwamitin shugabannin gudanarwar sa wanda zai dinga sa ido domin tabbatar da kare bayanan masu hulda da shi.

Hukumar ta kuma ce shugaban kamfanin Facebook da jami’an sa za su dinga gabatarwa hukumar shaida a kowanne watanni 3 cewar suna aiwatar da dokar kare bayanan asirin jama’a da kuma a karshen kowacce shekara.

Sai dai wasu daga cikin kwamishinonin hukumar guda biyu sun ki amincewa da matakin cin tarar kamfanin Dala biliyan 5, inda suka ce kudin yayi kadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.