Isa ga babban shafi
Duniya

Yan Sanda na tsare da wasu yan Adawa a Rasha

Zanga-zangar yan adawa a kasar Rasha
Zanga-zangar yan adawa a kasar Rasha REUTERS/Tatyana Makeyeva

Yan Sanda a Rasha sun kama sama da mutane dubu daya dake gudanar da zanga-zanga a jiya asabar.Masu zanga-zangar na fatan ganin an gudanar da sahihin zabe duk da mantsin lamba da gwamnatin kasar ke ci gaba da yi a siyasar kasar.

Talla

A makon da ya gabata Sama da mutane dubu 10.000 ne suka fito a wata zanga-zanga da ta gudana tsakiyar birnin Moscow inda suka bukaci ganin an gudanar da zaben kananan hukumomi masu inganci da kuma suka bi tafarkin Demokkuradiya a wannan kasa.

Gangamin na jiya asabar daga yan adawa na zuwa ne biyo bayan soke takarar da dama daga cikin yan takara da suka shigar da takardar su na neman kujerar Shugabancin da’irar birnin Moscow, zaben da za a yi a watan Satumbar shekarar bana.

Gwamnatin kasar ta aike da jami’an tsaro da za su bayar da kulawa domin kaucewa duk wani rikici ko tashin hankalin da kan iya biyo bayan wannan zanga-zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.