Isa ga babban shafi

An sake bude filin jiragen saman Hong Kong bayan zanga-zanga

Filin tashi da saukar jiragen saman Hong Kong, a ranar Litinin 12 ga watan Agusta 2019.
Filin tashi da saukar jiragen saman Hong Kong, a ranar Litinin 12 ga watan Agusta 2019. REUTERS/Thomas Peter

An sake bude filin sauka da tashin jiragen saman Hong Kong, bayan da dubban masu zanga-zanga suka mamaye filin jiragen saman tsawon yinin Litinin.Shugabar gwamnatin yankin na Hong Kong Carrie Lam ta yi gargadin cewa ci gaba da wannan tarzomar lamari ne da zai jefa yankin a cikin hali na rashin tabbas.

Talla

Bayan share tsawon makonni 10 suna gudanar da tarzomar nuna kin jinin gwamnatin Carrie Lam, a ranar litinin dubban masu rajin kare dimokuradiyyar suka mamaye filin jiragein saman Hong Kong, daya daga cikin filayen jiragen sama mafi hada-hada a duniya.

Tarzomar ta yi sanadiyyar dakatar da sauka da tashin daruruwan jirage a tsawon yinin na Litinin,lamarin da ya kara jefa kasuwar hannayen jari da sauran harkokin tattalin arziki cikin hali na rashin tabbas a yankin.

Mahukuntan China, kasar da ta karbi ragamar tafiyar da wannan yanki mai kwarya-kwaryan ‘yancin cin gashin kai daga hannun Birtaniya a 1997, sun fusata sakamakon kutse a filin jiragen saman, tare da bayyana wasu daga cikin masu zanga-zangar a matsayin ‘yan ta’adda

To sai dai duk da cewa an fara jigilar fasinja Talalatan nan, wasu daga cikin masu fafutukar sun bukaci a gudanar da wata zanga-zanga da marece  don mamaye filin jiragen saman, wanda a cewarsu ta hakan ne kaiwa za a tilasta wa mahukunta soke shirin tasa keyar wanda ake tuhuma da aikata laifi daga Hong Kong zuwa China domin fuskantar shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.