Isa ga babban shafi
Amurka- Rasha

Amurka ta yi gwajin makami mai linzami

Makami mai linzami da Amurka ta yi gwajin sa a jihar California
Makami mai linzami da Amurka ta yi gwajin sa a jihar California Scott Howe/Defense.gov

Makwanni kadan bayan janyewa daga yarjejeniyar hana gasar kera makaman nukiliya da ta kulla da Rasha a lokacin yakin cacar baka, karon farko Ma’aikatar Tsaron Amurka ta sanar da yin gwajin makami mai linzami da ke cin matsakaicin zango da ake harbawa a tudu.

Talla

Ma’aikatar tsaron Amurka Pentagon ta ce, wannan makami ne da ke cikin zangon kilomita 500, kuma an yi gwajin ne a barikin sojin ruwa da ke tsibirin San Nicolas kusa da birnin Los Angeles a jihar California.

Sanarwar ta ce, gwajin ya yi nasara sosai, yayinda Ma’aikatar Tsaron Kasar za ta yi amfani da darussan da ke ciki don kara inganta ayyuka da suka shafi kare Amurka.

Dominique Triquand, tsohon hafsa a rundunar tsaro ta Nato, ya ce baya ga tabbatar wa duniya cewa yarjejeniya ta INF da Amurka da Rasha suka kulla a shekarar 1987 ta daina aiki, gwajin na a matsayin sako ga kasashen China da kuma Rasha.

Shugaban Rasha Vladimir Putin da ke ziyara a Faransa, ya ce Amurka ce sanadiyyar rugujerwar yarjejeniyar ta INF, wadda ta hana gwajin irin wannan makami da ke iya cin zangon kilomita 500 zuwa 1,500, inda ya ce yanzu haka Rasha na cikin shiri don samar da wata sabuwar yarjejeniya da za ta maye gurbinta mai suna START lll, to sai dai ga alama Amurka ba ta cikin shiri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.