Isa ga babban shafi
Birtaniya

Majalisar Birtaniya ta amince da jinkirta Brexit

Firaministan Birtaniya, Boris Johnson
Firaministan Birtaniya, Boris Johnson PRU / AFP

‘Yan Majalisar Wakilan Birtaniya sun kada kuri’ar da za ta tirsasa wa Firaministan kasar, Boris Johnson neman karin wa’adin ficewar kasar daga gungun kasashen Turai, yayinda Firaministan ya bukaci gudanar da zaben gaggawa.

Talla

‘Yan majalisar wakilan Birtaniyar sun amince da matakin jinkirta ficewar da watanni uku nan gaba, matakin da  Johnson ya lashi takobin fatali da shi.

Sakamakon wannan kuri’ar ya dakile ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai ba tare da wata yarjejeniya ba, yayinda a yanzu za a mika batun ga Majalisar Dattawan domin samun amincewarta.

Sai dai a bangare guda, Firaminista Johsnon ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta kada wata kuri’ar amincewa da gudanar da zaben gaggawa bayan shirinsa na Brexit ya gamu da cikas.

A cewar Johnson, dole ne a gudanar da zaben gaggawar a ranar 15 ga watan Oktoba mai zuwa, yana mai cewa hanya daya ce ta rage domin ciyar da kasar gaba.

Johnson ya bayyana matakin da ‘yan majalisar suka dauka a matsayin abin takaici da kuma watsi da ayyukan da suka rataya a wuyansu.

A karkashin dokokin Birtaniya dai, dole ne kashi biyu cikin uku na mambobin majalsar dokokin su amince kafin gudanar da sabon zabe a kasar, abinda ke nufin cewa, Johson na bukatar jam’iyyar adawa ta Labour da ta mara masa baya kafin cimma muradinsa, amma kuma ‘ya’yan jam’iyyar na nuna turjiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.