Isa ga babban shafi

Trump ya tabbatar da mutuwar dan gidan Osama bin Laden

Oussama Ben Laden da Hamza Ben Laden
Oussama Ben Laden da Hamza Ben Laden DR

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya tabbatar da kisan Hamza bin Laden babban dan gidan Osama bin Laden ma’assasin kungiyar Jihadi ta Alqa’eda.

Talla

A cewar Trump, yanzu ne su ke da tabbacin mutuwar Hamza yayin wani sumame da aka kaddamar akan iyakar kasashen Afghanistan da Pakistan.

Tun cikin watan Yuli da farkon Agusta ne, wasu rahotanni suka tabbatar da mutuwar Hamza bin Laden tun a shekaru 2 da suka gabata, yayin sumame karkashin jagorancin Amurka, sai dai Trump da manyan Jami’an Amurka sun ki amincewa da batun a wancan lokaci.

Sai dai a yau Asabar yayin wani tyaron manema labarai da Trum,p yak ira ya tabbatar da mutuwar Hamza, sai dai bai fayyace rana da kuma lokacin da aka kashe mujahidin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.