Isa ga babban shafi
Saudiya

Saudiyya ta daina fitar da rabin adadin manta a kasuwar duniya

Hayaki a sararin samaniya sakamakon hari kan cibiyar kamfanin mai na Aramco a Abqaiq
Hayaki a sararin samaniya sakamakon hari kan cibiyar kamfanin mai na Aramco a Abqaiq Reuters

Ministan albarkatun mai na kasar Saudiyya Yerima Abdul aziz bin Salman ya ce kasar za ta dakatar da rabin man da take fitarwa a rana sakamakon harin da ‘yan tawayen Huthi da ke kasar Yemen suka kai wa cibiyoyinta na mai da ke Abqaiq da kuma Khurais a safiyar jiya asabar.

Talla

Ministan ya ce adadin man da kasar za ta daina fitarwa zai kai ganga milyan 5 da dubu 700 a rana.

Sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya zargi Iran a matsayinta na kasar da ke taimaka wa ‘yan tawayen na Huthi da hannu wajen kai wannan hari, yayin da a wata zantawa ta wayar tarho, shugaban Donald Trump ya ce Amurka za ta taimaka wa kasar ta Saudiyya domin kare cibiyoyinta na mai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.