Isa ga babban shafi

Babban taron Majalisar Dinkin Duniya zai maida hankali ga sauyin yanayi

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. ©REUTERS/Carlo Allegri

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da ke jagorantar zaman shekara-shekara na Majalisar ya ce zai yi iyakar kokarinsa wajen samun goyon bayan kasashe da nufin magance rikice-rikicen da duniya ke fuskanta ciki har da dumamar yanayi.

Talla

Yayin taron babban zauren na Majalisar Dinkin Duniya wanda zai tabo batutuwa da dama ciki har da dumamar yanayi da kuma rikice-rikicen kasashe, Sakatare Janar Antonio Gutteress ya ce iyakar kokarin da zai yi bai wuce fadakarwa tare da nuna alfanu ko kuma muhimmancin yakar matsalar ta dumamar yanayi ba.

Babban taron wanda zai kunshi akalla shugabannin kasashe 91 mataimaka 6, shugabannin gwamnatoci 45 baya ga ministocin kasase fiye da 40, zai tattauna tare da lalubo bakin zaren manyan matsalolin da duniya ke fuskanta.

A cewar Guterres mutane da dama na rayuwa cikin matsi da takura sanadiyyar rikice-rikicen kasashe da junansu yayinda dumamar yanayi ke barazana ga dubban rayuka matukar ba a dauki matakan da suka dace ba.

Ko cikin watan Mayu Guterres ya ziyarci yankuna da suka fuskanci tsananin zafi ciki har da tsibirin Bahamas inda ya ke cewa akwai bukatar kasashe su fara dabbaka alkawarin da suka daukarwa yarjejeniyar yanayi ta Paris a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.