Isa ga babban shafi
Duniya

Taron Majalisar Dinkin Duniya na 74 a New York

Antonio Guterres, tareda daliba Greta Thunberg, yayin ganawa a Majalisar Dinkin Duniya
Antonio Guterres, tareda daliba Greta Thunberg, yayin ganawa a Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Carlo Allegri

Kimanin shugabannin kasashen Duniya 60 zasu  halarci taron majalisar Dinkin Duniya na 74 a birnin New York,a jajubirin taron Shugabanin sun mayar da hankali zuwa batun dumamar yanayi don tattabar da kokarin kasashen Duniya wajen aiwatar da yarjejeniyar birnin Paris kan canji da dumamar yanayi, a dai-dai lokacin da ake fuskantar zafin rana da ba’a taba ganin irin sa ba.

Talla

A yau litinin jawabin bude taron sakatare janar na majalisar Dinkin Duniya Antonia Guterres, wanda yace ya ziyar ci yankunan Duniya daban-dan kuma ya shaida barazanar da duniyar ke ciki kan dumamar yanayi, ya kuma bukaci kasashen da su aiwatar da alkawaran da aka cimma a yarjejeniyar birnin paris na kasar Faransa a shekarar 2015.

A daya geffen Greta Thunberg, daliba mai shekaru 16 dake rajin kare muhalli, baza su taba yafewa Shugabanin kasashen duniya ba kan halin ko in kula da suka nuna kan yanayi.

Dalibar ta bayana cewa "Duniya na tasowa, kuma za’a samu canji ko kuna so ko kuna adawa a kai”.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.