Isa ga babban shafi
Sahel-MDD

Duniya ta gaza shawo kan matsalar ta'addanci a Sahel

Wasu daga cikin dakarun tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel
Wasu daga cikin dakarun tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel AFP/Stephane de Sakutin

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa cewar kasashen da ke Afrika ta Yamma da manyan kasashen duniya sun gaza wajen magance barazanar 'yan ta’adda a yankin Sahel wanda yanzu haka ke bazuwa zuwa kasashen da ke yankin tekun Guinea.

Talla

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce, kungiyoyin 'yan ta’adda da ke da alaka da Al Qaeda da IS sun fadada yaduwarsu a yankin Sahel a cikin wannan shekara, musamman a kasashen Mali da Burkina Faso.

Yayin gudanar da wani taro na kasashen da matsalar yankin Sahel ta shafa a Majalisar Dinkin Duniya, Guterres ya ce, tabbas a fada wa kowa gaskiya, domin ba a samun nasara a yakin da ake fafatawa, duk da damuwar da mahalarta taron ke bayyanawa game da yaduwar tashin hankalin.

Sakataren ya ce, a watan Yulin da ya gabata, mayakan IS sun fadada aikinsu a Afrika ta Yamma, abin da ya sa ya zama wajibi ga kasashen da ke yankin su kara kaimi wajen daukar matakan soji fiye da wanda ake yi yanzu.

A na shi martani, shugaban Burkina Faso, Roch Marc Kabore ya ce, kasashen G5 Sahel ba za su iya magance wannan matsala ba, kuma hakan na iya sa rikicin ya kara yaduwa.

Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean Yves Le Drian ya ce, taron ba wai na kara yawan sojoji a Yankin Sahel ba ne, sai dai karfafa rundunar da ke yankin domin fuskantar duk wani kalubale.

Kasar Faransa yanzu haka na da sojoji 4,500 a ynakin, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke da dakaru 15,000 da suka hada da 'yan sanda da kuma sojoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.