Isa ga babban shafi
Afghanistan

Yau shekaru 18 da Amurka ta fara yaki a Afghanistan

Wasu daga cikin dakarun Amurka dauke da kayayyakin yaki a Afghanistan
Wasu daga cikin dakarun Amurka dauke da kayayyakin yaki a Afghanistan REUTERS/Ahmad Nadeem

Yau ake cika shekaru 18 da fara yakin Afghanistan, lokacin da Amurka ta kaddamar da hare-hare a shekarar 2001, sakamakon farmakin ranar 11 ga watan Satumba da aka kai birninta na New York wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan dubu 3,yayin da aka zargi kungiyar Al Qaeda da kitsa harin.

Talla

Dakarun Amurka sun kifar da gwamnatin Taliban ta wancan lokaci da ta ki mika shugaban Al Qaeda, Osama bin Laden cikin makwanni bayan harin , amma kuma hakan bai kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 18 ana fafatawa ba, wanda ya zama yaki mafi tsayi da Amurka ta tsinci kan ta a ciki.

Bayan kwashe wadannan shekaru ana fafatawar da ta kai ga mutuwar dubban mutane da kuma dakarun Amurka da na Kungiyar Tsaro ta NATO, a karshe dai, Amurkar ta shiga tattaunawa da kungiyar Taliban domin ganin sun ajiye makamansu da zummar maido da zaman lafiya a kasar ta Afghanistan.

Yakin da ake fama da shi a kasar ya gurgunta tattalin arzikinta, yayin da iyaye ke cire ‘ya’yansu daga makarantu domin shigar da su aikin kwadagon da zai rika kawo musu kudin sayen abinci.

Wasu matasa na zaman kashe wando sakamakon rashin aikin yi, abin da ke tilasta musu balaguro zuwa kasashen ketare domin samun ingantacciyar rayuwa ko kuma su shiga cikin kungiyar Taliban wadda za ta rika biyan su kudaden albashi.

Hukumar Kula da Yawan Al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kashi 42 na al’ummar Afghanistan yara ne ‘yan kasa da shekaru 14, yayin da Asusun Tallafa wa Ilimin Kananan Yara na Majalisar ya ce, akalla yara miliyan 3.7 akasarinsu mata, ba sa zuwa makaranta a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.