Isa ga babban shafi

Zanga-zangar dumamar yanayi ba ta yi armashi a sassan duniya ba

Wasu masu zanga-zangar dumamar yanayi a Faransa
Wasu masu zanga-zangar dumamar yanayi a Faransa JACQUES DEMARTHON / AFP

Masu Zanga zangar bukatar ganin hukumomi sun dauki kwararan matakan kare muhalli a kasashen duniya, sun yi arangama da Yan Sanda a birane daban daban saboda matakan da suka dauka na tare hanya da kuma gudanar da jerin gwano, daga cikin tsarin da suka yi na bijirewa dokoki na makwanni biyu.

Talla

Rahotanni sun ce zanga zangar ta jiya ba ta samu fitowar mutane sosai a garuruwa daban daban ba, amma kuma ta yi tasiri a kasashe da dama sakamakon jerin gwanon da akayi a kasashen Turai da wani sashe na Asia da Afirka da kuma Arewacin Amurka.

An nuna hotunan wasu masu zanga zangar wadanda ke daure kawunan su da sarka a jikin motoci da kuma gine gine, yayin da wasu ke kwanciya a tituna.

Wannan dai ne karo na biyu da aka shiryamakamanciyar zanga-zangar da ta gudana a sassan duniya rana guda, don farkar da shugabannin game da illar da ke tunkaro al'umma kan gaza daukar mataki yaki da dumamar yanayi.

Masana dai na ci gaba da gargadin cewa kalubalen dumamar yanayin na shirin kai wa wani mataki da duniya baza ta iya magance matsalarsa ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.