Isa ga babban shafi
Turkiya-Syria

Farmakin Turkiya ya hallaka mutane a Syria

Yankin Akcakale da Turkiya ta yi lugudan wuta da zummar fatattakar mayakan Kurdawa
Yankin Akcakale da Turkiya ta yi lugudan wuta da zummar fatattakar mayakan Kurdawa EUTERS/Murad Sezer

Akalla mutane biyar sun rasa rayukansu da suka da wani jariri, yayin da 46 suka jikkata sakamakon hare-heren da Turkiya ke ci gaba da kaddamarwa kan mayakan Kurdawa na Syria. Farmakin ya kuma tilasta wa mutane sama da dubu 60 kaurace wa gidajensu kawo yanzu.

Talla

Hare-haren baya-bayan nan sun kashe wani jariri dan kasar Syria mai watanni tara da haihuwa da kuma wani farar hula da ke aiki a ofishin karbar haraji da ke yankin Akcakale.

‘Yan jaridar Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP sun ce, da idanunsu, sun shaida yadda aka yi ta luguden wuta kan ginin gwamnati da ke Akcakale .

Kazalika an kaddamar da makamancin wannan farmaki a yankin Ceylanpinar.

Yankunan biyu dai, na kusa da garuruwan Tal Abyad da Ras Al-Ain da ke kan iyakar Syria da Turkiya.

Turkiya dai na cewa, tana kaddamar da hare-haren ne da zummar fatattakar mayakan Kurdawa da take kallo a matsayin ‘yan ta’adda, sannan kuma ta kafa tudun-mun-tsira don samun damar mayar da ‘yan gudun hijirar Syria gida.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci Turkiyar da ta gaggauta kawo karshen luguden wutarta a yankin arewacin Syria, yana mai cewa ci gaba da farmakin zai kara farfado da karsashin kungiyar ISIS.

ma Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a cikin wata sanarwar da ya fitar, ya gargadi cewa, farmakin Turkiyar wani yunkuri ne na share kabilar Kurdawa daga doron kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.