Isa ga babban shafi
Amurka-G7

Taron G7 na badi ba zai tattauna matsalar dumamar yanayi ba- Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Leah Millis

Fadar shugaban Amurka ta ce batun sauyin yanayi baya daga cikin batutuwan da shugabannin kasashen G7 za su tattauna a wajen taron da za suyi a Amurka cikin shekara mai zuwa a wajen wanda shugaba Trump zai karbi bakoncinsa a filin wasan kwallon golf mallakinsa.

Talla

Mai rike da mukamin Babban Hafsa a fadar shugaban kasa, Mike Mulvaney ya tabbatar da matsayin na gwamnatin Amurka wanda ke cigaba da nuna yadda shugabancin Trump ke adawa da matsalar.

Kasar Amurka da China ke haifar da rabin sinadaren da ke gurbata muhalli a fadin duniya.

Tun bayan hawan mulkin Donald Trump ya cire Amurkan daga cikin yarjejeniyar yanayi ta Paris da ke neman kasashen duniya su rage sinadaran da ke gurbata muhalli.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.