Isa ga babban shafi
Syria-Amurka

Amurka ta tabbatar da mutuwar al-Baghdadi

Jagoran mayakan IS Abubakar al-Baghdadi da Amurka ta tabbatar da mutuwarsa. Al-Baghdadi ya bayyana ne a wani sabon bidiyo da ya fitar na ranar 29 ga Afrilun 2019.
Jagoran mayakan IS Abubakar al-Baghdadi da Amurka ta tabbatar da mutuwarsa. Al-Baghdadi ya bayyana ne a wani sabon bidiyo da ya fitar na ranar 29 ga Afrilun 2019. AFP / AL-FURQAN MEDIA

Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da mutuwar jagoran kungiyar IS Abubakar Al-Baghdadi, bayan farmakin da dakarun Amurkan suka kai kan maboyarsa dake wani kauye Baricha lardin Idlib a Syria.

Talla

Shugaban Amurka da kan sa ne ya sanar da mutuwar Al-Baghdadi a wani taron manema labarai a fadar White House.

Shugaba Trump dake magana gaban manema labarai ya ce al-Baghdadi ya kashe kansa ne ta hanyar tarwatsa damarar bam din dake jikinsa tareda wasu yaran sa guda uku a cikin wani rami.

A karshe shugaban na Amurka Donald Trump ya mika godiya ga kasashen Turkiyya, Rasha, Syria da Iraqi.

Gabannin bayyana kai farmakin, shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a shafinsa na twitter cewar, wani muhimmin al’amari ya auku.

Amurka ta dade tana farautar jagoran kungiyar ta IS, gami da alkawarin bada ladan dala miliyan 25 ga wanda ya taimaka da bayanan gano maboyarsa.

A baya dai an sha kuskuren bayyana ikirarin samun nasarar halaka shi.

Abubakar al-Baghdadi mai shekaru 48, dan Iraqi ne, wanda ya jagoranci mayakan Al-Qaeda a kasar, tare da daukar alhakin hare-haren bam masu yawan gaske kan mabiya akidar shi’a da Sunni a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2013.

A 2013 ya sanar da raba gari da Al-Qaeda gami da kafa kungiyar IS da nufin kafa daularsa a yankunan dake kan iyakar Syria da Iraqi, yunkurin da yayi sanadin halaka dubban jama’a.

A shekarar 2014 al-Baghdadi ya bace, bayan da kawancen dakarun da Amurka ke jagoranta suka bayyana ikirarin kashe shi a lokuta daban daban.

Sai dai cikin watan Afrilun 2019, al-Baghdadi ya bayyana cikin wani sabon bidiyo, inda yake kira ga mabiyansa da su zage damtse wajen kai hare-haren daukar fansar ‘yan uwansu da aka halaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.