Isa ga babban shafi
Amurka

Trump Junior ya caccaki abokan adawar Shugaba Trump

Trump Junior da Shugaban kasar Donald Trump
Trump Junior da Shugaban kasar Donald Trump rfi

Dan Shugaban Amurka Donald Trump, ya gabatar da wani littafi da ya rubuta wanda ya caccaki abokan adawar mahaifin sa, kana kuma yace shima yana nazari kan shiga takarar zabe nan gaba.

Talla

Littafin da aka yiwa suna ‘Triggered: How the Left Thrives on Hate and Wants to Silence US’, dan shugaban ya kare manufofin mahaifin sa, yayin da ya caccaki kafofin yada labaran Amurka da kuma abokiyar adawar mahaifin sa, Hillary Clinton.

Tuni littafin ya zama na uku cikin wadanda aka fi saye a jerin litattafan Amazon, yayin da Shugaba Trump ya bukaci mutane miliyan 66 da rabi dake bin sa ta kafar twitter da su gaggauta sayen nasu domin karantawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.