Isa ga babban shafi
Asiya

Fafaroma ya bukaci daina amfani da makamin nukiliya

Fafaroma Francis a garin Nagasaki
Fafaroma Francis a garin Nagasaki REUTERS/Remo Casilli

Shugaban Mabiya darikar Katolika na duniya, Fafaroma Francis ya bukaci kawo karshen mallakar makamin nukiliya a duniya, yayin ziyarar aikin da ya kai Nagasaki da Hiroshima dake kasar Japan.

Talla

Bayan ganawa da wasu daga cikin mutanen da suka sha da kyar bayan Amurka ta jefa musu makaman nukiliyar a shekarar 1945, wadanda suka bayyana irin ukubar da suka gani, Fafaroma ya bayyana amfani da makamin ayau a matsayin laifuffukan cin zarafin bil Adama.

Yoshiko Kajimoto, wadda ke da shekaru 14 lokacin da aka jefa musu makamin ranar 6 ga watan Agustan shekarar 1945, wanda yayi sanadiyar kashe mutane akalla 140,000 ta shaidawa Fafaroman cewar bayan jefa bama baman wurin yayi duhu, kuma babu abinda suke ji sai warin rubabben kifi.

Cikin hawaye Kajimoto tace babu wanda yake a duniya da zai iya tuna irin wancan yanayi mai tada hankali, inda ta bukaci daina amfani da makamin nukiliyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.