Isa ga babban shafi
Libya-Berlin

Taron sasanta rikicin Libya ya kankama a Berlin

Jami'an tsaron Jamus a wajen taron sasanta rikicin Libya da ke gudana a birnin Berlin.
Jami'an tsaron Jamus a wajen taron sasanta rikicin Libya da ke gudana a birnin Berlin. REUTERS/Hannibal Hanschke

Kasashen duniya da ke halartar taron sasanta rikicin Libya can a birnin Berlin karkashin jagorancin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun sha alwashin ganin diflomasiyya ta taka rawa wajen magance rikicin kasar, dai dai lokacin da shugaba Emmanuel Macron ke ganin tsagaita wuta bazai yiwu ba har sai Turkiya ta janye matakin aikewa da dakaru don tallafawa gwamnatin Firaminista Fayez Al-sarraj.

Talla

Taron na kwana guda wanda ke samun halartar shugabannin kasashen Turkiya, Rasha, Birtaniya da kuma sakataren harkokin wajen Amurka na kokarin tattaunawa don kawo karshen rikicin na Libya bayan da aka shiga wata na 9 da kaddamar da farmakin Khalifa Haftar a kokarinsa na kwace iko da birnin Tripoli.

A bangare guda shugaban shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya yi gargadin cewa dole ne babban kwamandan Sojin Libyan da ke rike da manyan yankunan kasar Khalifa Haftar ya kawo karshen dabi’arsa ta mamayar yankunan kasar baya ga garkuwa da jami’an gwamnati matukar ana fatan dorewar yarjejeniyar zaman lafiyar kasar da ake shirin kullawa.

A ganawar Erdogan da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, shuagban na Turkiya ya nanata bukatar ganin lallai Haftar ya mutunta ka’idojin da yarjejeniyar za ta kunsa.

Shima dai Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce kasarsa a shirye ta ke ta aike da kwararru don taimakwa wajen ganin an samu wanzuwar zaman lafiya a kasar.

Taron dai na samun halartar Firaministan na Libya da kuma Khalifa Haftar bangarorin biyu masu fada da juna a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.