Isa ga babban shafi
Isra'ila-saudiya

'Yan Isra'ila za su fara ziyartar Saudiya

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu Abir Sultan/Pool via REUTERS

Isra’ila ta bai wa ‘yan kasarta ‘yancin ziyartar Saudiya domin gudanar da ayyukan ibada da kuma harkokin kasuwanci, abin da ake kallo a matsayin sabon matakin karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Talla

A karon farko Ministan Cikin Gidan Isra’ila, Aryeh Deri ya sanya hannu domin amince wa Yahudawa da Musulman kasar yin balaguro kai tsaye daga kasar zuwa Saudiya.

A can baya dai, Isara’ilawa ba su da ‘yancin ziyartar Saudiya kai tsaye daga kasar har sai sun fara isa Jordan kafin daga bisani su kama hanyar Saudiya.

Kodayake kawo yanzu Saudiya ba ta ce uffam ba a hukumance game da batun, amma wasu alamu na baya-bayan nan sun nuna cewa, dankon zumunci ya dada karfafa tsakanin kasashen biyu.

Ko a ranar Lahadin da ta gabata, Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya jinjina wa Shugaban Kungiyar Kasashen Musulmi ta Duniya mai cibiya a birnin Makkah, Mohammed al-Issa saboda ziyarar da ya kai Poland domin halartar taron cika shekaru 75 da ‘yantar da Yahudawa daga sojojin Nazai a sansanin ihunka banza na Auschwitz.

Ana ganin cewa, kasashen biyu sun kara kusanci da juna ne saboda yadda tasu ta zo daya wajen hamayya da kasar Iran a yankin Gulf.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.