Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

MDD za ta bi doka wajen warware rikicin Isra'ila da Falasdinawa

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Sergio Perez

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yace hakkin Majalisar ne cigaba da kare dokokin duniya a rikicin dake gudana tsakanin israila da Falasdinu, kwanaki bayan shugaba Donald Trump ya gabatar da shirin san a sasanta rikicin bangarorin biyu.

Talla

Yayin ganawa da manema labarai, Guterres ya ce matsayin Majalisar Dinkin Duniya a fayyace yake dangane da dokokin duniyar da kuma matsayin Falasdinu.

Guterres ya ce har yanzu babu abinda ya sauya dangane da matsayin su na samun kasashe biyu tsakanin Israila da Falasdinu akan iyakokin shekarar 1967.

Wannan matsayi na Guterres da Majalisar Dinkin Duniya yaci karo da shirin shugaba Trump wanda ya mallakawa Israila Birnin Kudus da kuma halarta mata mamaye wasu yankuna da suka hada da tuddan Golan da Yankin Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.