Isa ga babban shafi
Kimiya

An harba kumbo zuwa duniyar rana don binciken kwa-kwaf

Shu'umin kumbon da zai gudanar da bincike a duniyar rana.
Shu'umin kumbon da zai gudanar da bincike a duniyar rana. ESA/ATG medialab; Sun: NASA/SDO/ P. Testa (CfA)

An harba wani shu’umin kumbo zuwa duniyar rana domin gudanar da binciken kwa-kwaf game da taswirar rana da kuma yanayinta. Masana kimiya sun ce, ana sa ran kumbon zai tattaro muhimman bayanai game da hucin rana da kuma iskar da ke kewayawa a kusa da ita, yayin da aka makala masa kyamarori da wasu na’urorin da za su taimaka masa wajen tattaro bayanai.

Talla

An harba Kumbon ne daga jihar Florida karkashin hadin guiwar Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Turai ESA da kuma Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka NASA, inda ake sa ran kumbon zai shafe tsawon shekaru tara ko fiye da haka yana gudanar da aikinsa matsawar bai gamu da matsala ba.

Masana kimiya na fatan zurfafa fahimtarsu kan yadda yanayin rana ke sassauyawa akai akai, lura da cewa, wani lokacin ta na watso biliyoyin kwayoyin halittun zarra tare da kanannade sararin samaniyar mayen karfe, abin da ke yin tarnaki ga hanyoyin sadarwar rediyo a wannan duniya tamu, wani lokacin ma ta lalata turaken lantarki.

Bayanai sun nuna cewa, akwai tazarar kilomita miliyan 150 tsakanin duniyarmu da duniyar rana, amma wannan kumbon zai tsaya ne daga tazarar kilomita miliyan 42 tsakanisa da ranar, yayin da aka makala masa wasu shu’uman na’urorin sanyaya shi domin jurewa tsananin zafin da zai fuskanta.

Sai dai kumbon zai rika ja baya duk bayan watanni shida domin kara murmurewa kafin ya sake kusantar ranar don ci gaba da bincikensa.

Masana kimiya sun ce, duniyar rana ta rubanya duniyarmu har sau miliyan 1 da dubu 300, yayin da harskenta ke isowa kan doran kasa cikin minti 8 da zaran ta bullo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.