Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta kaddamar da sabon makami mai linzami

Wasu nau'ukan makamai masu linzami mallakin kasar Iran
Wasu nau'ukan makamai masu linzami mallakin kasar Iran AFP

Dakarun Juyin-Juya Halin Iran sun kaddamar da wani sabon makami mai linzami da ke cin matsakaicin zango da aka sarrafa da sabbin injina masu saukin isar da sako sararin samaniya.

Talla

Sanarwar dakarun ta nuna cewa sabon makamin na Raad-500, an sarrafa shi ne da injinan Zoheir marasa nauyi.

Sabon makamin na Raad-500 wanda ke da rabin nauyin Fateh-110 mai tafiya a karkashin kasa da ka samar a 2002, na cin karin zangon kilomita 200 fiye da Fateh mai tafiyar kilomita 300.

Kazalika sanarwar rundunar dakarun na Iran ta nuna yadda kasar ta kuma kaddamar da wasu sabbin fasahohin injinan Salman da ta samar da sinadarai guda dana Fateh wadanda za su tallafa wajen gaggauta kai sakon tauraron dan Adam.

Rahotanni sun bayyana cewa, sabuwar fasahar makamin na Raad-500 za ta saukaka nauyi da kuma saurin makami mai linzami baya ga saukin sarrafawa da kuma araharsa wajen mallaka.

A cewar shugaban dakarun Juyin-Juya Halin, Manjo Janar Hossein Salami yayin kaddamar da sabon makamin mai linzami, za a sanya sabuwar fasahar cikin ilahirin makaman da kasar ta mallaka masu linzami da za su saukaka amfani da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.