Isa ga babban shafi
China

Matakin China ya yi tasiri kan yaki da Coronavirus

Jami'an kiwon lafiya a China
Jami'an kiwon lafiya a China REUTERS/Rodrigo Urzagasti

China ta sanar da gagarumar raguwar yaduwar cutar Coronavirus, abin da ke nuna irin tasirin matakan da gwamnatin kasar ke dauka na dakile annubar, yayin da adadin mutanen da cutar ta kashe ya karu a kasashen Japan da Koriya ta Kudu.

Talla

Hukumomin kiwon Lafiya na China sun sanar da raguwar yaduwar Coronavirus hatta a lardin Hubei da ya kasance makyankyasar wannan cuta.

Kodayake kawo yanzu an tabbatar da mutuwar jumullar mutane dubu 2 da 118 a China kadai, inda kuma dubu 74 suka kamu da cutar a kasar, ba ya ga daruruwan mutane daban da cutar ta harba a wasu kasashen duniya 25.

Baya ga China, mutane 11 ne cutar ta lakume a sassan duniya, inda mutane 3 suka mutu a Japan da suka hada da wasu tsoffi da suka haura shekaru 80 bayan an killace su a jirgin yawon bude ido a gabar ruwan Yokohama.

Kasar Koriya ta Kudu ta sanar da mutun na farko da cutar ta lakume, sannan adadin wadanda suka kamu da ita ya kai 104.

A jiya Laraba ne, kasar Iran ta sanar da mutuwar mutane 2, kuma a karon farko kenan da cutar ta yi kisa a yankin gabas ta tskiya.

Sauran kasashen da cutar ta yi kisa sun hada da Faransa da Philippines da Taiwan da kuma Hong Kong.

Gwamnatin China ta ce, tsaurarran matakan da take dauka da suka hada da killace miliyoyin mutane a lardin Hubei tare da takaita zirga-zirga a biranen kasar, sun fara yin tasiri wajen rage bazuwar Coronavirus ko kuma Covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.