Isa ga babban shafi
Isra'ila

Netanyahu na shirin gina wa Yahudawa gidaje a Kudus

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu Debbie Hill/Pool via REUTERS

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana shirin gina dubban gidaje ga Yahudawa a Gabashin Birnin Kudus, wurin da aka ware domin zama babban birnin kasar Falasdinu, matakin da ke zuwa kasa da makonni biyu kafin babban zaben Isra'ila.

Talla

A wani sakon bidiyo da ya aika wa al’ummar kasar ranar Alhamis, Netanyahu ya bayyana cewar yana dauke da babban sako ga Yahudawa kan shirin gina sabbin gidaje 2,200 a wurin da ya kira Har Homa.

Yankin da Netanyahu ya kira Har Homa, tun a shekarar 1997 ya fara gina shi, a lokacin wa’adin gwamnatinsa da ya gabata.

Netanyahu ya ce, ya amince da wannan ginin da kasashen duniya ke adawa da shi, domin bunkasa shi, ta yadda ya yi kiyasin karuwar al’ummar Har Homa daga dubu 40 zuwa dubu 50, a lokacin da za a kammala sabbin gidajen.

Benjamin Netanyahu ya kuma sanar da gina wani sabon matsuguni mai dauke da dubbun gidaje a Givat Hamatos, a kusa da Beit Safafa na yankin Falasdinawa da ke gabashin birnin Kudus.

A nasu martani Falasdinawa sun bayyana matakin a matsayin yunkurin samun goyan bayan masu tsattsauran ra’ayi kafin zaben da za ayi na Isra'ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.