Isa ga babban shafi

MDD ta bukaci shirin kafa kasar Falasdinu

Falasdinawa masu zanga-zanga adawa da matakin Amurka na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila
Falasdinawa masu zanga-zanga adawa da matakin Amurka na amincewa da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila REUTERS/Ali Hashisho

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kasashen duniya su mutunta shirin kafa kasar Falasdinu a matsayin hanya daya tilo da za’a warware rikicin Gabas ta Tsakiya.

Talla

Sanarwar da kasar Belguim dake shugaban kwamitin ta gabatar, yace kwamitin sulhu ya bayyana goyan bayan sa na ganin an samu kasashe biyu Isarila da Falasdinu dake zama kafada da kafada akan iyakokin da kasashen duniya suka amince da shi a shekarar 1967.

Kwamitin ya bukaci bangarorin biyu da su kaucewa daukar duk wani mataki da zai hana samun dawamammen zaman lafiya a yankin na Gabas ta Tsakiya.

Kasashe 14 daga cikin 15 dake kwamitin sulhu suka goyi bayan sanarwar, yayin da Amurka ita kadai taki sanya hannu akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.