Isa ga babban shafi
Amurka

Amurkawa za su shiga yanayi mai tsauri-Trump

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Jonathan Ernst

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi Amurkawa da su shirya tinkarar makwanni 2 mafi tsauri dangane da yaduwar cutar COVID-19 wadda yanzu haka ta kashe mutane sama da 41 a duniya.

Talla

Alkaluma sun bayyana cewar Amurka ta fi kowacce kasar duniya samun masu dauke da cutar, yayin da ta kashe mutane 4,076 kuma sama da kasha 40 a Birnin New York.

Kasar Amurka ta zarce China wajen samun adadin masu dauke da wannan annobar da ta kashe mutane sama da 41 a duniya, yayin da hukumomin kasar suka bada alkaluman mutane 189,510 da suka kamu da ita.

Babban jami’in kula da lafiyar kasar Anthony Fauci, ya karfafa wa jama’ar kasar gwuiwa dangane da shawo kan cutar duk da yanayin da ake ciki.

Fauci ya ce, abinda za su gani nan gaba, shi zai ba su damar jajircewa a cikin kwanaki da dama masu zuwa.

Shi kuwa shugaba Donald Trump da a baya ya yi watsi da illar cutar da kuma shirin bayyana sake bude harkokin yau da kullum kafin bikin Easter, ya gargadi Amurkawa cewar makwanni biyu masu zuwa nan gaba, suna da matukar sarkakiya a gare su.

"Ina son kowanne Ba'amurke ya shiryawa kwanaki masu tsauri da ke zuwa nan gaba, zamu shiga cikin yanayi mai sarkakiya, sannan muna da fatar cewar za mu fara ganin haske kan lamarin, amma wannan zai zama abu mai ciwo, makwanni biyu mafi tsanani." Inji shuagba Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.