Isa ga babban shafi
Coronavirus

Coronavirus ta zama bala'i mafi muni ga duniya- MDD

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres RFI

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana annubar coronavirus a matsayin bala’i mafi muni da ya afka wa duniya tun bayan yakin duniya na II, yana mai cewa, annubar za ta iya haddara rikici a doran-kasa.

Talla

Shugabannin Hukumar Samar da Abinci da Bunksa Aikin Gona ta Duniya da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya har ma da Hukumar Kasuwanci ta Duniya sun gargadi cewa, al’ummar duniya na fuskanatr barazanar karancin abinci muddin mahukunta suka gaza shawo kan wannan annuba.

Cutar dai ta lakume rayukan mutane fiye da dubu 43 a sassan duniya, yayin da ta harbi sama da mutane dubu 865 da 970 a kasashe 186 tun bayan barkewarta a cikin watan Disamban bara a China.

An fitar da sabbin alkaluman ne a tsakiyar ranar yau Laraba, inda a Italiya aka samu asarar rayuka dubu 12 da 428, Spain dubu 9 da 053, yayin da a Amurka aka samu mamata dubu 4 da 081. Sai kuma Faransa da ta rasa mutane dubu 3 da 523.

Wadannan kasashe hudu sun zarta China wadda ta yi asarar mutane dubu 3 da 312 duk da cewa, cutar ta coronavirus ta samo asali ne daga kasar, yayin da Iran ta rasa mutane dubu 3 da 36.

Birtaniyar ta bada rahoton mutuwar mutane 563 a yau Laraba kawai, kuma a karon farko kenan da kasar ke samun alkalumam mamatan da suka zarta 500, amma a jumulce mutane dubu 2 da 52 suka mutu a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.