Isa ga babban shafi
Coronavirus

Halin da duniya ke cikin kan cutar Coronavirus

Kasashen duniya da dama sun killace mutane a gida don hana yaduwar coronavirus
Kasashen duniya da dama sun killace mutane a gida don hana yaduwar coronavirus REUTERS/Jeenah Moon

Cutar coronavirus ta lakume rayukan mutane fiye da dubu 43 a sassan duniya, yayin da ta harbi sama da mutane dubu 865 da 970 a kasashe 186 tun bayan barkewarta a cikin watan Disamban bara a China.

Talla

An fitar da sabbin alkaluman ne a tsakiyar ranar yau Laraba, inda a Italiya aka samu asarar rayuka dubu 12 da 428, Spain dubu 9 da 053, yayin da a Amurka aka samu mamata dubu 4 da 081. Sai kuma Faransa da ta rasa mutane dubu 3 da 523.

Wadannan kasashe hudu sun zarta China wadda ta yi asarar mutane dubu 3 da 312 duk da cewa, cutar ta coronavirus ta samo asali ne daga kasar, yayin da Iran ta rasa mutane dubu 3 da 36.

A can Birtaniya kuwa, wani matashi mai shekaru 13 ya rasa ransa bayan gwaji ya nuna cewa, ya kamu da coronavirus kamar yadda asibitin da ya yi jinya ya sanar, kuma danginsa sun bayyana cewa, marigayin bai yi fama da wata cuta ba baya ga coronavirus.

Har ila yau, Birtaniyar ta bada rahoton mutuwar mutane 563 a yau Laraba kawai, kuma a karon farko kenan da kasar ke samun alkalumam mamatan da suka zarta 500, amma a jumulce mutane dubu 2 da 52 suka mutu a kasar.

Ita ma kasar Senegal ta samu mutun na farko da ya mutu a kasar sakamkon wannan annuba, wato Pape Diouf, tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Olympique Marseille mai shekaru 68, yayin da kasar Burundi ta sanar da bullar cutar a karon farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.