Isa ga babban shafi
Amurka

Coronavirus ta kashe Amurkawa kusan 900 a rana guda

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi Amurkawa cewa za su fuskanci makwanni biyu masu tsauri saboda coronavirus
Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi Amurkawa cewa za su fuskanci makwanni biyu masu tsauri saboda coronavirus REUTERS/Leah Millis

A karon farko cutar coronavirus ta kashe Amurkawa 884 a rana guda, amma a jumulce mutane dubu 5 da 116 annubar ta kashe a kasar kamar yadda Jami’ar Johns Hopkins ta rawaito.

Talla

Jami’ar ta ce, yanzu haka Amurka ce ta fi yawan masu dauke da cutar a duk fadin duniya, inda take da mutane dubu 215 da 417 da suka harbu da ita.

Abdurrahman Dandi Abarshi mazaunin Amurka ne kuma ya yi wa RFI hausa karin bayani kan halin da suke ciki, yana mai cewa, Amurkawa na kokawa game da kayan  gwaje-gwajen cutar coronavirus a kasar..

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren muryar Abdurrahman Dandi Abarshi

Muryar Abdulrahman Dandi Abarshi daga Amurka

Tun da farko, shugaban kasar Donald Trump ya gargadi Amurkawa da su shirya tinkarar makwanni 2 mafi tsauri dangane da yaduwar cutar COVID-19.

"Ina son kowanne Ba'amurke ya shirya wa kwanaki masu tsauri da ke zuwa nan gaba, zamu shiga cikin yanayi mai sarkakiya, sannan muna da fatar cewar za mu fara ganin haske kan lamarin, amma wannan zai zama abu mai ciwo, makwanni biyu mafi tsanani." Inji shuagba Trump.

Amurka ta zarce China wajen samun yawan masu dauke da cutar, amma ba ta kai Italiya da Spain ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.