Isa ga babban shafi
Faransa-Coronavirus

Coronavirus ta lakume Faransawa fiye da 500 a kwana guda

Jami'an yaki da cutar Coronavirus a Faransa
Jami'an yaki da cutar Coronavirus a Faransa AFP

Faransa ta sanar da mutuwar mutane 509 da suka kamu da cutar COVID-19, adadi mafi girma da aka taba samu tun bayan barkewar annobar wadda yanzu haka ta kashe mutane 4,030 a kasar.

Talla

Sama da  mutane dubu 24 ne ke kwance a asibitocin Faransa sakamakon kamuwa da cutar, kuma fiye da dubu 6 daga cikinsu na kwance ne a sashen kula da wadanda ke cikin halin rai–kwakwai-mutu-kwakwai a cewar wani bayani daga Ma’aikatar Lafiyar kasar.

Wannan adadi na wadanda suka mutu a asibitoci ne kawai, ban da na gidajen kula da tsofaffi da kuma wadanda suka mutu a gidajensu.

Adadin wadanda aka tabbatar sun harbu ya karu da dubu 4 da dari 861,  sai dai akwai da dama da ba a samu tantance su ba saboda karancin kayan gwaji.

Ma’aikatar Lafiyar Faransa, ta ce wadanda ke sashen kula da marasa lafiyar da yanayinsu ya tsananta sun zarce adadin da sashen ke iya dauka.

Tun daga ranar 17 ga watan Maris ne hukumomi suka killace Faransawa da zummar dakile yaduwar cutar COVID 19 da tuni ta zame wa duniya babbar annoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.