Isa ga babban shafi
Coronavirus

Masu coronavirus sun zarce miliyan 1

Majalisar Dinkin Duniya ta ce nan kusa masu coronavirus za su kai miliyan 1 a duniya
Majalisar Dinkin Duniya ta ce nan kusa masu coronavirus za su kai miliyan 1 a duniya PETER PARKS / AFP

Alkaluman mutanen da suka kamu da cutar coronavirus sun zart miliyan 1 a sassan duniya, a daidai lokacin da annubar ke mummunar barna a nahiyar Turai, yayin da Amurka ta sanar da mutuwar jariri mai makwanni shida da haihuwa sakamakon wannan cuta.

Talla

Cutar coronavirus ta lakume rayukan dubun dubatan mutane a sassan duniya da suka hada da kusan mutane dubu 1 da ta kashe a cikin sa’o’i 24 a Spain kadai duk da cewa, kusan rabin al’ummar duniya na kulle a gidajensu don dakile ci gaban yaduwar wannan bala’i.

Tun bayan barkewar wannan cuta daga China a karshen shekarar bara, ta harbi mutane sama da dubu 940 da suka hada da sabbin mutane kusan dubu 500 a nahiyar Turai kadai, baya ga rayuka dubu 47 da ta lakume.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, wannan annuba na ci gaba da yaduwa cikin saurin gaske.

A bangare guda, Amurka ta ce, wani jariri mai makwanni shida da haihuwa ya mutu a kasar bayan kamuwa da coronavirus, abin da ya sa ya zamo mafi karancin kwanakin haihuwa da wannan cuta ta kashe a tarihin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.