Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Mu dai babu ruwanmu da coronavirus- Korea ta Arewa

Shugaba Kim Jong-un na Korea ta Arewa tare da wasu mukarrabansa
Shugaba Kim Jong-un na Korea ta Arewa tare da wasu mukarrabansa KCNA/via REUTERS

Korea ta Arewa ta bayyana cewa, ko kadan ba ta fama da cutar coronavirus duk da yadda annubar ke ci gaba da karade lungu da sako na duniya tare da harbar mutane kusan miliyan 1 baya ga kashe kimanin dubu 46.

Talla

Tun a cikin watan Janairu ne kasar ta Korea ta Arewa mai makamin nukiliya ta rufe kan iyakokinta jim kadan da bullar cutar a makwabciyarta wato China, yayin da ta kafa wasu tsauraran dokokin yaki da cutar tun a tashin farko.

Darektan Hukumar Yaki da Annuba a Shalkwatan Yaki da Annubar Gaggawa, Pak Myong Su, ya jaddada cewa, matakan da suka dauka sun yi tasiri.

Pak ya ce, babu mutun ko guda da wannan cuta ta coronavirus ta kama a Korea ta Arewa.

Kodayake masana kiwon lafiya sun bayyana cewa, cutar ka iya shafar kasar musamman saboda rashin ingancin tsarin kiwon lafiyarta, yayin da babban kwamandan sojin Amurka a Korea ta Kudu, Robert Abrams ya ce, yana da yakinin cewa, wannan cuta ta shiga Korea ta Arewar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.