Isa ga babban shafi
Coronavirus

Mutane dubu 200 sun warke daga cutar coronavirus

Wasu daga cikin likitiocin da ke kula da masu dauke da cutar coronavirus a Italiya.
Wasu daga cikin likitiocin da ke kula da masu dauke da cutar coronavirus a Italiya. REUTERS/Flavio Lo Scalzo

A kalla mutane dubu 200 aka tabbatar sun warke daga annobar cutar COVID-19 a sassan duniya, daga cikin mutane kusan miliyan guda da suka kamu da cutar wadda ta hallaka mutane kimanin dubu 47.

Talla

Bayanan baya-bayan nan kan cutar ta COVID-19 ko kuma coronavirus sun nuna cewa, duk da kasancewarta mai saurin yaduwa, kaso mai yawa na wadanda suka kamu da ita, na iya warkewa, inda a China, kasar da cutar ta samo asali, aka samu  jumullar mutane dubu 76 da 238 da suka warke daga cutar ta corona, cikin mutum dubu 81 da 554 da suka kamu, yayin da mutum dubu 3 da 312 suka mutu.

Italiya wadda ke matsayin kasa mafi yawan masu dauke da cutar a duniya, a kalla mutane dubu 16 suka warke daga cikin mutane dubu 110 da 238 masu dauke da cutar, yayin da Spain ke da jumullar mutane dubu 10 da 3 da suka warke.

A Faransa an samu mutane dubu 4 da 32 cikin mutum dubu hamsin da 6 da 989 da suka kamu.

Iran kasar da cutar ta fi yi wa barna a Gabas ta Tsakiya, yanzu haka tana da jumullar mutane dubu 16 da 711 da suka warke daga corona cikin mutum dubu hamsin da dari 468 da suka kamu, kodayake cutar ta kashe dubu 3 da 160 a kasar.

Kasashen Amurka da Canada na da adadin mutane dubu 7 da 138 da suka warke daga cutar, cikin mutum dubu dari 2 da 26 da dari 247 da suka kamu.

A Najeriya, kasa mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika, yanzu haka mutum 9 suka warke daga cutar ta COVID-19 cikin mutum 174 da cutar ta kama ta kuma kashe biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.