Isa ga babban shafi
Coronavirus

Coronavirus ta sake hallaka daruruwan Faransa a kwana guda

Masu yaki da coronavirus a Faransa
Masu yaki da coronavirus a Faransa SEBASTIEN BOZON / AFP

A Faransa, adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon annobar Covid-19, sun kai 471 a cikin sa’o’i 24, yayin da wadanda suka kamu da cutar suka zarta dubu 26 a fadin kasar.

Talla

Daraktan kiwon lafiya a Faransa Jerome Salomon wanda ya bayyana wadannan alkalumma, ya ce illahirin mutanen 471 sun mutu ne a kan gadajen asibiti, abin da ke nufin cewa akwai wadanda suka mutu a cikin gidajensu bayan sun kamu da cutar.

Jerome Salomon ya ce lura da wadannan alkalumma, adadin wadanda suka mutu a fadin kasar ta Faransa bayan sun harbu da wannan cuta sun tashi zuwa mutane 5,387 a halin yanzu, musamman ma idan aka hada da wadanda suka rasa rayukansu a gidajen kula da tsofaffi.

Alkalumman da aka tattara a ranar Alhamis, na nuni da cewa a wadannan gidaje kawai, Covid-19 ta kashe tsofaffi 884 a sassan kasar.

A jimilce dai adadin wadanda suka kamu da wannan annoba a Faransa sun kai dubu 26, kuma dubu 6 da 399 na cikin matsanancin hali saboda na’ira ce ke taimaka masu domin yin numfashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.