Isa ga babban shafi
Coronavirus

Kusan Faransawa 600 sun sake mutuwa a kwana guda

Jami'an yaki da cutar Coronavirus a Faransa
Jami'an yaki da cutar Coronavirus a Faransa JEAN-CHRISTOPHE VERHAEGEN / AFP

A yammacin wannan Juma’ar Faransa ta sake bada rahoton da ke cewa, coronavirus ta kashe mata mutane 588 a asibitoci, kuma wannan adadi shi ne mafi muni da kasar ta gani tun bayan barkewar cutar a kasar.

Talla

Jumullar mutane dubu 5 da 91 ne coronavirus ta kashe a asibitocin Faransa kamar yadda babban jami'in kiwon lafiya a kasar, Jerome Solomon ya shaida wa manema labarai.

Wannan adadin bai hada da alkaluman mutanen da cutar ta kashe a gidajen kula da tsofaffi ba da ke Faransa, yayin da babban jami'in kiwon lafiyar ke cewa, a kalla mutane dubu 1 da 416 ne cutar ta kashe a ire-iren wadannan gidaje.

A cewar jami'in, an samu raguwar mutanen dake kiran layukan gaggawa don neman agaji, amma hakan ba yana nufin cewa, cutar na raguwa ba ne a cewarsa.

Tun a cikin a ranar 17 ga watan Maris ne Faransa ta kafa dokar hana zirga-zirga don dakile yaduwar cutar ta coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.