Isa ga babban shafi
Coronavirus

Adadin mamatan coronavirus ya zarta dubu 70

Jami'an yaki da cutar Coronavirus a Faransa
Jami'an yaki da cutar Coronavirus a Faransa REUTERS

Ya zuwa tsakiyar ranar wannan Litinin, cutar covid-19 ta kashe mutane fiye da dubu 70 a kasashen duniya 191, yayin da mutane sama da miliyan 1 da dubu 200 suka kamu da ita.

Talla

Annobar coronavirus ta kashe mutane sama da dubu 50 a kasashen Turai kadai da suka hada da mutane dubu 15 da 877 a Italiya, kasar da wannan annoba ta fi barna a nahiyar.

Spain ce kasa ta biyu wajen samun asarar rayuka, inda mutanenta dubu 13 da 55 suka mutu, yayin da Faransa ta yi asarar mutane dubu 8 da 78, sai Birtaniya mai mutane dubu 4 da 934.

Kodayake kwanaki uku kenan a jere da ake samun raguwar mace-mace a Spain sakamakon wannan annoba, inda a wannna Litinnin kadai, kasar ta rasa mutane 637, adadi mafi kankanta cikin kwanaki 13.

Biliyoyin mutane na ci gaba da zaman gida na dole a sassa daban daban na duniya sakamakon matakan da gwamnatoci suka dauka na takaita zirga-zirga da zummar kawo karshen wannan annoba.

Sai dai a bangare guda, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bukaci gwamnatocin kasashen da su dauki matakan kare mata a daidai lokacin da rahotanni ke cewa, rikice-rikicen ma’aurata sun kazanta a sassan duniya tun lokacin da aka sanya dokar hana fita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.