Isa ga babban shafi
Coronavirus

Coronavirus ta lakume rayuka kusan dubu 80

Coronavirus ta yi duniya dabaibayi
Coronavirus ta yi duniya dabaibayi indiatimes

Alkaluman Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 ya kusan 80,000, yayin da wadanda suka kamu da ita suka zarce miliyan guda da dubu 300.

Talla

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, alkaluman  sun bayyana cewar mutane miliyan guda da dubu 310, 930 suka kamu da annobar COVID-19 a kasashe 191 tun bayan gano cutar a watan Disamban bara a kasar China, yayin da akalla 249,700 suka warke, bayan ta kashe  79,139.

Daga ranar Lahadin da ta gabata zuwa jiya Litinin, mutane 5,005 suka mutu, yayin da aka samu sabbin wadanda suka kamu da cutar 66,187 a fadin duniya, kuma Amurka ke matsayi na farko da mutane 1,209 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, sai Faransa da ita ta rasa mutane 833 da suka mutu cikin kwana guda, yayin da Spain ta yi asarar mutane 637.

Kasar Italiya ta fi yawan mutanen da suka mutu, inda suka kai 16,523, sai Spain mai mutane 13,055, sai Amurka mai 10,389, sannan Faransa mai mutane 8,911.

A nahiyar Turai kawai mutane 52,498 suka mutu, sai Amurka da Canada da ke da 10,728, sai Asia mai mutane 4,265, sai Gabas ta Tsakiya mai mutane 3,948, sai Amurka ta Kudu da Yankin Carribean da ke da 1,188, sannan Afirka mai mutane 467.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.